Muna Neman Gafarar Premier Rediyo-Kwamishinan 'Yan sandan Kano




Rundunar 'yan sandan  jihar Kano ta nemi gafarar dan jaridar dake aiki da Premier Radio mai suna Muhammad Bello Dabai wanda guda daga cikin ma'aikatanta ya ciwa zarafi tare da hana shi gudanar da aikin sa.

A yammacin wanana rana ta Talata ne dai kwamishinan 'yan sandan ya turo tawaga gidan Rediyon Premier dake unguwar Nassarawa GRA don ganawa da mahukuntan gidan wannan gidan Rediyo  don neman gafarar su kan wannan aika aika da ta faru a jiya litinin 19/12/2022.

Kwamishinan 'yan sandan na Kano Mamman Dauda ya aike da tawaga ta musamman zuwa gidan Rediyo Premier karkashin mataimakin kwamishinan yan sanda ACP Abubakar Modibbo.

Kwamishinan yan sandan na Kano ya aike da tawagar ne bayan ya bada hakuri ta wayar tarho ga hukumar gudanarwa ta Premier Radio.

A cikin tawagar da kwamishinan yan sandan  ya aike har da jami'in da ya aikata aika-aikar, inda ya gurfana don neman afuwar Muhammad Bello Dabai.

Yan jarida dai na fuskantar cin zarafi daga wurin jami'an yan sanda a sassan Najeriya dama wasu sassan kasashen duniya.

Rundunar yan sanda ta Kano ta ce zata gudanar da bincike don daukar mataki kan dan sandan da ya ci zarafin dan jarida Muhammad Bello Dabai.

0/Post a Comment/Comments