KISAN BUDURWA: Kotu Ta Saurari Shaidun Karshe Kan Kisan Da Dan China Ya Yiwa Budurwar sa a Kano



Babbar kotun  jiha dake miller road karkashin mai shari'a Sunusi Ado Ma'aji ta ci gaba da sauraran shaida na 6 da ɓangaren masu gabatar da ƙara duka kawo kotun a yau, a shari'ar da akewa ɗan china Mr Frank Geng Quorang na tuhumar kashe budurwasa, Ummul Kulsum Sani Buhari.

Lauyoyin Gwamnati karƙashin Jagorancin Barrister A'isha Mahmoud sun gabatar da


shaidansu na ƙarshe Ɗansanda Aminu Aliyu dake aiki a Chaji Office na Ɗorayi Babba.

Aminu Aliyu ya bayyana kotun cewa a ranar 16/9/2022 Frank Geng Quarong suka samu sabani da shi da Ummita wanda ake zarginsa da yin amfani da wuka wajen hallaka ta inda ta mutu daga bisani.

Yace Koda samun labarin ne DPO ɗinsa ya kira shi a waya, suka kai ta asibiti amma likita ya tabbatar da rasuwarta a ranar.

Bayan haka ne aka tafi da Frank Quarong zuwa ofishin yan sanda na Dorayi Babba wanda ya bayar da bayanan abunda ya faru da ƙashin kansa, ba tare da tursasawa ba.

Har aka kammala daukar bayanan sannan aka bawa Frank ya karanta kuma ya saka hannu.

To sai dai lauyan wanda ake zargi Barista Balarabe Muhammad Dan-Azumi ya bayyana wa kotun cewa tursasawa wanda ake zargi aka yi har ya saka hannu akan takkadar bayanan yan sanda, wato statement if Police.

Sai dai duk da sukan da lauyoyin suka yiwa juna  Alkalin kotun mai shari'a Sunusi Ado Ma'aji ya karbi bayanan shaidar na karshe da lauyoyin gwamnati suka gabatar.

0/Post a Comment/Comments